Ni fa na gama gamsuwa cewa; 'Yan Kungiyar Salafiyyun, Malamansu da jahilansu sun jahilci hakikanin Khawarijawa.
Ai su Khawarijawa Annabi (saw) ne da bakinsa ya bayyana siffofinsu a fili, daga ciki ya nuna cewa:
1- Sun fi kowa Sallah da Azumi da karatun Alkur'ani, amma maras amfani.
2- Suna "Muruqi" wato suna fita daga Addini.
4- Suna kashe Musulmai su bar Kafirai.
* Saboda haka ne Annabi (saw) ya zarge su zargi mai tsanani, har ya kwadaitar a kan yakarsu da kashe su.
To in ka ce: Malamanmu da suka shahara da da'awar Sunna a Nigeria suna kan tafarkin Khawarijawa to fa kana nufin suna da wadancan siffofi da Annabi (saw) ya yi bayani. Don haka hukuncinsu shi ne a yake su a kashe su.
To abin tambaya a nan; yaushe Malamai masu da'awar Sunna a Nigeria suka siffantu da wadancan siffofi har da za a danganta su da Khawarijawa?!
Saboda haka da wannan za ka san cewa; duk wanda ya jingina Malamanmu Ahlus Sunna a Nigeria ga Khawarijawa to ya jahilci su waye Khawarijawa saboda tsabar zafin kai, ko kuma kawai zaluntarsu yake son yi, saboda tsantsar zaluncin da kungiyar ta Salafiyyun ta shahara da shi.
Saboda haka maganar wani jahili ko azzalumi da hukuncinsa na bidi'antar da Malamai Ahlus Sunna abin jefawa ne a kwandon shara.
Comments
Post a Comment