SHAIKH JA'AFAR (R) DA 'YAN BOKO AQIDA
A kokarinsu na batanci wa Marigayi Shaikh Ja'afar da Da'awarsa ta Sunna da mabiya Sunnan a yau, 'Yan Boko Aqida suna danganta shi da Marigayi Muhammad Yusuf wanda ya kafa Kungiyar Boko Haram, inda suke cewa; ai Muhammad Yusuf din almajirin Shaikh Ja'afar ne, don su nuna cewa; Muhammad Yusuf ya dauki tunanin Boko Haram ne daga Shaikh Ja'afar din. Alhali wasu da suka san Muhammad Yusuf kuma suka san Malam Ja'afar, sun tabbatar da cewa; asali Muhammad Yusuf tafiyar Harkar Gwagwarmayar kifar da Gomnati ya fara yi a karkashin jagorancin Ibrahim El- Zakzaky, wanda daga baya ya yi masa tawaye tare da sauran wadanda suka yi tawaye, bisa zargin shigar da Shi'anci cikin tafiyar, wadanda suka zama Kungiyar JTI, wacce take alakanta kanta da Kungiyar Ikhwan ta Misra. Wanda sai daga baya ne Muhammad Yusuf ya hadu da Malam Ja'afar a bisa tafiyar Sunna ko Salafiyya.
A baya - bayan nan, tun bayan bayyanar wani faifan audio na wata huduba ta Marigayi Shaikh Ja'afar wacce a cikinta ya yi bayanin munafurcin wani marubuci a wancan lokaci, 'Yan Boko Aqida sun kara kaimi wajen yin batanci wa Marigayin da Da'awarsa ta Sunna. Abu na karshe da suka yi shi ne kokarin alakanta Marigayin da wani Mulhidi "A Humanist. An Atheist. An ardent Anti-Theist. Angry at callous religions. Posts, with humor".
To duka wannan yunkuri ne kawai na gajiyayye kasasshe, saboda duk wanda ya san hakikanin Da'awar Malam Ja'afar ta Sunna ya san babu maganar Gwagwarmayar kifar da Gomnati a cikinta, balle daukan makami a kan al'ummar Musulmi da halasta jininta kamar yadda yake a wajen Boko Haram. Haka kuma duk wanda ya san Malam Ja'afar to tabbas ya san matsayarsa a kan Da'awar Muhammad Yusuf, ya yi masa nasiha da fadakarwa, ya yi masa gargadi, har ya yi masa raddi a bayyane.
A takaice, duk mai adalci ya san cewa; Da'awar da Muhammad Yusuf ya fito da ita ta Haramta Boko, gyauro ce ta tafiyarsa da ya yi a Harkar Gwagwarmayar kifar da Gomnati a karkashin jagorancin Zakzaky.
Saboda haka, hudubar da Malam Ja'afar ya yi a kan wancan marubuci a wancan lokaci ba ya yi ta ne a dalilin rigima da take tsakaninsu a kan hakkinsa na kashin kansa ba, a'a, ya yi ta ne a dalilin kasancewar wancan mutumin yana fada da Addini, don haka in har bai tuba ya dena ba, to babu abin da zai canza maganganun da Malam Ja'afar ya fada a kansa a cikin hudubar tasa.
Amma kasancewar Muhammad Yusuf ya hadu da Malam Ja'afar, har ma ake cewa; almajirinsa ne, wannan ba abin mamaki ba ne, saboda kowa ya san cewa; Khawarijawan farko sun fito ne daga cikin mabiya Sayyyidina Aliyu bn Abi Dalib (ra), amma hakan bai sa an ce: daga wajensa suka koyi Khawarijancin ba. Kamar yadda kowa ya san cewa; Munafukai wadanda za su kasance a karkashin wuta suna cikin wadanda suke tare da Annabi (saw), amma babu Musulmin da zai ce: shi ya koya musu munafurcin. Saboda haka ba mamaki a ce: Muhammad Yusuf ya bi Malam Ja'afar, amma hakan kawai ba zai sa a ce: a wajensa ya dauki tunanin na Boko Haram ba.
Babban abin da ya fi muni da rashin tunani kuma shi ne alakanta Malam Ja'afar da Mulhidi!
Saboda haka, kokarin da 'Yan Boko Aqida suke yi na batanci wa Shaikh Ja'afar da Da'awarsa ta Sunna ta hanyar alakanta shi da Boko Haram da kuma Mulhidai shi yake kara tabbatar mana da cewa; kare hakki da neman 'yanci da 'Yan Boko Aqida da iyayen gijinsu Turawa suke rayawa duka karya ne da yaudara, saboda a aikace su suka fi kowa take hakki da tauye 'yancin masu riko da Addini wadanda suka saba hanyarsu
Comments
Post a Comment