Shin da Gaske Prof. Maqari ne ya Kirkiri Wadannan Darajoji?
Wani ya ce:
Kabarin Annabi (saw) ya fi Al'arshi daraja.
To lallai duk wanda ya fadi wannan ya jahilci cewa; ita falala ba a tabbatar da ita da dalili na hankali, ko Qiyasi na hankali. Ana tabbatar da falala da daraja ne ta hanyar Nassi. Saboda ita falala da daraja a cikin halitta "Isdifa'i" ne, wato tsantsar zabi ne daga Allah. Allah ya ce:
{وربك يخلق ما يشاء ويختار، ما كان لهم الخيرة} [القصص: ٦٨].
{Ubangijinka yana halittar abin da ya ga dama kuma ya zabi abin da ya ga dama (ya fifita shi). Bai kasance suna da zabi ba}.
Wannan yake nuna Allah shi kadai yake zabi ya ba da falala da daraja, ba shi da abokin tarayya a cikin haka.
To, ta yaya ka san Allah ya zabi Daren Maulidi ya fifita shi a kan Daren Lailatul Qadr?
Ta yaya ka san Allah ya zabi Kabarin Annabi (saw) ya fifita shi a kan Al'arshi?
Babu hanyar da za ka san haka sai ta hanyar Nassi.
To ina Nassin?
Mu abin da muka sani a Nassi shi ne:
Allah ya siffanta Al'arshi da siffofin girma da daraja. Allah ya ce:
{العرش العظيم}.
{العرش الكريم}.
{العرش المجيد}.
Kuma Allah ya ware shi, ya kebance shi a tsakanin sauran halittu ya daukaka a samansa. Allah ya ce:
{الرحمن على العرش استوى} [طه: ٥].
Wannan yana nuna girman darajarsa, saboda shi ne halitta mafi girma da daukaka da dadewa, yana sama da komai. Daga shi sai Allah Madaukakin Sarki a cikin daukakarsa.
Don haka kai da ka fifita Kabarin Annabi (saw) a kansa, wa ya gaya maka hakan?
Wa ya ce maka ana sanin falala da daraja da tsurar hukuncin hankali?
Haka Daren Lailatul Qadr, Allah ya yabe shi, ya ce dare ne mai albarka:
{إنا أنزلناه في ليلة مباركة} [الدخان: ٣].
Kuma ya ce: Daren Lailatul Qadr ya fi wata dubu.
Mala'iku suna yawan sauka a cikinsa.
Akwai aminci a cikinsa har hudowan alfijir.
To kai da ka ce: Daren Maulidi ya fi falala, wa ya gaya maka, a ina ka samo hakan?
Shin ba ka san ba a kirkiran wata falala da daraja ma wani abu ba, sai da Nassi?
Don haka mu dai abin da Allah ya ba mu labari shi ne Falala da Darajar Al'arshi, da Falala da Darajar Daren Lailatul Qadr, kuma ba mu ga haka a kan Kabarin Annabi (saw) ba, haka Daren Maulidi, balle mu ga an fifita su a kan wadancan.
A takaice, ba a kirkirar falala da daraja da molon-ka, a'a, dole sai da Nassi. Saboda ba a sanin falalar abu ta hanyar Qiyasin hankali.
Saboda haka wadancan maganganu guda biyu za su shiga babin kirkiran karya ma Allah.
Da shar'anta Shari'a ba tare da iznin Allah ba.
Da kuma karyata Allah cikin labarin da ya ba mu na falala da darajar Al'arshi da Daren Lailatul Qadr.
Kuma shirka ne ma Allah a cikin zabinsa, saboda Allah shi kadai ne mai zabi, kamar yadda shi kadai ne mai halitta.
Comments
Post a Comment