'Yanci a Muslunci shi ne halin da mutum zai kasance mai kaskantar da kai ga mahaliccinsa, cikin mallakar tasarrufin kansa, yana mai zabi cikin aiyukansa matukar bai keta hakkin Allah ko hakkin wani daga cikin bayin Allah ba.
Saboda haka ne Muslunci ya ba wa mutum cikakken 'yanci, ta yadda Allah ya halicci mutun ya ba shi 'yanci a fagage masu yawa na rayuwarsa.
Allah Madaukaki ya halicci mutum ya ba shi 'yanci da iko da zabi da ganin dama wajen aikata dukkan aiyukansa da zai iya aikatawa, sawa'un aiki ne mai kyau ko kuma aiki ne mummuna. Mutum yana da daman ya bar mummunan aiki don ya samu sakamako da tsira daga azaba a Ranar Lahira, kamar yadda yake da dama da zabi da ikon aikata kyakkyawa don ya samu kyakkyawan sakamako a kansa.
Kamar haka Muslunci ya ba ma kowane mutum 'yancin kansa, ta yadda yana da daman yin abin da ya so, kuma ya mallaki duk abin da ya so matukar bai keta hakkin Allah ko hakkin mutane ba. Da wannan Muslunci ya haramta yi ma wani ta'addanci a kansa ko mutuncinsa ko dukiyarsa ko kowane irin hakki daga cikin hakkokinsa da ya cancance su.
Duk wani fage da ake magana a kan 'yanci za ka samu Muslunci ya bayar da 'yanci ga mutane 'yanci da zai zama musu maslaha a rayuwarsu ta Duniya da ta Lahira.
Amma 'yanci da Mulhidai cikin Turawa da 'Yan Falsafa da 'Yan Boko Aqida suke rayawa za ka samu a bisa hakika ba 'yanci ba ne, kawai halakar da kai ne, da kuma tauye ma wasu hakki. Musamman in ka dauki abin da suke kira gare shi na 'yancin kai, ko 'yanci mata, za ka samu yana tattare da tarin manyan barna masu girma a rayuwar mutum ko danne hakkin mata, ko kuma suna kai wa ga miyagun aiyuka masu lalata hankali da kwakwalwa, ko ta'addanci a kan mutane.
Comments
Post a Comment