Skip to main content

Posts

Showing posts from March, 2023

Can we implement the qāʿidah (ie: rules of) al-Jarḥ wa ʿl-Taʿdīl on everyone who errs or there is a detailed addressing whereas some people are advised and others are criticized?”

 Can rules of al-Jarḥ wa ʿl-Taʿdīl (ie: praise and criticism) be implemented on everyone who errs? (Question): “Can we implement the qāʿidah (ie: rules of) al-Jarḥ wa ʿl-Taʿdīl on everyone who errs or there is a detailed addressing whereas some people are advised and others are criticized?” (Muqbil b. Hādī al-Wādiʿī): Praise is to Allah, and may Allah send praise and peace upon our Prophet Muḥammad, all of his household and his companions. I bear witness that no deity is worthy of worship except Allah and I bear witness that Muḥammad is His messenger and His servant. To proceed: Verily al-ʿulamāʾ wa ʿl-ṣaḥābah (ie: the scholars and the companions) before them used to commit mistakes, And Shaykh al-Islām Ibn Taimiyyah may Allah have mercy on him mentioned some of that in his treatise “Rafʿ al-Malām ʿan al-Aʾimmah al-Aʿlām”. And he mentioned errors of Abū Bakr then ʿUmar then ʿUthmān then ʿAlī, may Allah be pleased with them all, And mentioning these mistakes takes a long time so we ...

MENENE HAKIKANIN MUSLUNCI, KUMA WANENE MUSULMI NA HAKIKA?

  MENENE HAKIKANIN MUSLUNCI, KUMA WANENE MUSULMI NA HAKIKA? Shaikhul Islami Ibnu Taimiyya (r) ya ce: الإسلام هو أن يستسلم لله، لا لغيره؛ فيعبد الله ولا يشرك به شيئا، ويتوكل عليه وحده، ويرجوه، ويخافه وحده، ويحب الله المحبة التامة، لا يحب مخلوقا كحبه لله، بل يحب لله، ويبغض لله، ويوالي لله، ويعادي لله. فمن استكبر عن عبادة الله لم يكن مسلما، ومن عبد مع الله غيره لم يكن مسلما. وإنما تكون عبادته بطاعته؛ وهو طاعة رسله؛ فمن يطع الرسول فقد أطاع الله النبوات لابن تيمية (1/ 417) "Muslunci shi ne mutum ya mika wuya ga Allah ba ma waninsa ba, sai ya bauta ma Allah kar ya yi masa shirka ya hada shi da komai, ya dogara ga Allah shi kadai, ya yi fatan alheri a wajensa, ya ji tsoronsa shi kadai, kuma ya so Allah cikakkiyar soyayya, kar ya so wani halitta kamar sonsa ga Allah, a'a, ya so halittan don Allah, ya ki shi don Allah, ya jibince shi don Allah, ya yi gaba da shi saboda Allah. Duk wanda ya yi girman kai ga bautar Allah to bai zama musulmi ba, haka duk wanda ya bauta ma wanin Allah tare ...
  AHLUS SUNNA A TSAKIYA SUKE A GAME DA HANKALI A game da hankali, tafarkin Ahlus Sunna Mabiya Salaf matsakaici ne tsakanin masu wuce iyaka game da shi, da kuma masu sakaci da wofintar da shi. 'Yan Falsafa (Philosophers) da kuma da yawa daga cikin mabiya "Ilmul Kalam" da 'Yan Boko Aqida (Intellectuals) suna fifita hankali suna kai shi matsayin da bai kai ba, ta yadda suke sanya shi a matsayin tushen daukan ilmukansu, ta yadda suke mayar da Qur'ani da Sunna da Imani a matsayin mabiya ga hankalin. A daya hanun kuma, 'Yan Darikun Sufaye sun saba ma wadannan, ta yadda suka wulakanta hankali, suka zarge shi suka aibanta shi, ta yadda suke ganin cewa; ba a samun matsayi da daukaka sai ta hanyar jefar da hankali. Shi ya sa Sufayen suke tabbatar da abubuwan da hankali yake karyatawa. Suke yabon maye da hauka da sauran yanayi na gushewar hankali, saboda a wajensu sai mutum ya isa wani matsayi na gushewar hankali kafin ya isa zuwa ga Hakika ko "Fana'i" da s...

HABA MALAM Saleh Kaura, BA DAGA ALJIHUNKA MUKE BUKATA BA!

  HABA MALAM Saleh Kaura, BA DAGA ALJIHUNKA MUKE BUKATA BA! Abu ne sananne a Addinin Muslunci cewa; Allah ya wajabta wa Muminai yin Jihadi na yakar kafirai saboda Allah, a karkashin jagorancin Shugaban Daular Muslunci, idan akwai karfi da iko a kan haka, kuma matukar Maslahar yinsa tana da rinjaye. A kan haka Ahlus Sunna suke har tashin Alkiyama, saboda Allah ya ce: {كُتِبَ عَلَيْكُمُ الْقِتَالُ وَهُوَ كُرْهٌ لَكُمْ وَعَسَى أَنْ تَكْرَهُوا شَيْئًا وَهُوَ خَيْرٌ لَكُمْ وَعَسَى أَنْ تُحِبُّوا شَيْئًا وَهُوَ شَرٌّ لَكُمْ وَاللَّهُ يَعْلَمُ وَأَنْتُمْ لَا تَعْلَمُونَ } [البقرة: 216] "An wajabta muku YAKI alhali shi abun ki ne gare ku...". Shaikhul Islam Ibnu Taimiyya yana bayanin Aqidar Ahlus Sunna a cikin "Al-Wasidiyya" sai ya ce: ويرون إقامة الحج والجهاد والجمع والأعياد مع الأمراء أبرارا كانوا أو فجارا ويحافظون على الجماعات. مجموع الفتاوى (3/ 158) "Ahlus Sunna suna da Aqidar tsayar da aikin Hajji da JIHADI da Sallar Juma'a da Eidi a KARKASHIN SHUGABANNI, sawa...

MANUFAR SHAR'ANTA IBADOJI A CIKIN JAM'I.

  MANUFAR SHAR'ANTA IBADOJI A CIKIN JAM'I. AL- SHAIKH ABDURRAHMAN BN NASIR AL- SI'IDIY YA CE: "YANA DAGA CIKIN UMURNIN ALLAH MAFI GIRMA, DA SHARI'O'I SAUKAKKU DAGA SAMA, DA WASIYOYIN ANNABI (SAW); MUTANE SU HADU A KAN RIKO DA IGIYAR ALLAH CIKIN HADIN KAI, DA HADUWAR KALMAR MUSULMAI WAJE DAYA, DA HADIN KANSU DA DUNK'ULEWARSU WAJE GUDA". YA CE: "YANA DAGA CIKIN NASIHA MAFI GIRMA WA MUSULMAI YIN KOKARI WAJEN HADA ZUKATANSU, DA HADA KANSU DA KUMA HANASU RARRABUWA". YA CE: "ALLAH DA MANZONSA SUN YI UMURNI DA HADUWAR MUSULMI CIKIN JAM'I A IBADOJI MASU YAWA, KAMAR A AIKIN HAJJI DA SALLAR IDI DA SALLAR JUMA'A DA SALLAR JAM'I (SALLOLIN FARILLA 5), SABODA A CIKIN HADUWAR TASU ZA A SAMU SOYAYYA A TSAKANINSU DA SADA ZUMUNCI DA RASHIN KAURACE MA JUNA. KUMA ALLAH DA MANZONSA SUN YI HANI A KAN GIBA (CIN NAMA) DA ANNAMIMANCI DA GULMA DA KAURACE MA JUNA DA HA'INCI DA HASADA DA RIK'O DA MAKAMANTANSU, DUKA SABODA HAKAN ZAI KAWO BARNA A...

TA'ASSUBANCI SHI NE HAKIKANIN HIZBIYYANCI (KUNGIYANCI ABIN ZARGI)

  TA'ASSUBANCI SHI NE HAKIKANIN HIZBIYYANCI (KUNGIYANCI ABIN ZARGI) Sau da yawa za ka samu mutane sun ware kansu, suna bin wani malami ko wasu malamai 'yan tsiraru, suna kulla soyayya da kiyayya a kansu, amma ba sa yarda a kirasu da sunan kungiya, ma'ana a kullum suna inkari ga wanda ya siffantasu da kungiyanci, alhali a bisa hakika kungiyanci abin zargi suke yi matukar akwai TA'ASSUBANCI A TARE DA SU. Don fahimtar wannar mas'ala zamu yi nazarin wasu maganganun malamai guda biyu, malami da almajirinsa: Shaikhul Islami Ibnu Taimiyya (r) ya ce: دين المسلمين مبني على اتباع كتاب الله وسنة رسوله وما اتفقت عليه الأمة فهذه الثلاثة هي أصول معصومة، وما تنازعت فيه الأمة ردوه إلى الله والرسول، وليس لأحد أن ينصب للأمة شخصا يدعو إلى طريقته، ويوالي عليها ويعادي غير النبي صلى الله عليه وسلم ولا ينصب لهم كلاما يوالي عليه ويعادي غير كلام الله ورسوله وما اجتمعت عليه الأمة، بل هذا من فعل أهل البدع الذين ينصبون لهم شخصا أو كلاما يفرقون به بين الأمة، يوالون على ذلك الكلام أو تلك النسبة ...

WAJIBI NE MU NISANCI DUK ABIN DA ZAI JANYO KIYAYYA A TSAKANIN AHLUS SUNNA

  WAJIBI NE MU NISANCI DUK ABIN DA ZAI JANYO KIYAYYA A TSAKANIN AHLUS SUNNA Imamu Muslim ya ruwaito: عن أنس، أن النبي صلى الله عليه وسلم، قال: «لا تحاسدوا، ولا تباغضوا، ولا تقاطعوا، وكونوا عباد الله إخوانا» صحيح مسلم (4/ 1983) Daga Anas (ra) ya ce Annabi (saw) ya ce: "Kar ku yi Hasada a tsakaninku, kar ku yi Kiyayya a tsakaninku, kar ku yanke alaka da juna, ku zama bayin Allah 'yan uwan juna". Shaikhul Islam ya ce: وقرن في الحديث الأول الحسد بالبغضاء؛ لأن الحاسد يكره أولا فضل الله على ذلك الغير؛ ثم ينتقل إلى بغضه؛ فإن بغض اللازم يقتضي بغض الملزوم فإن نعمة الله إذا كانت لازمة وهو يحب زوالها وهي لا تزول إلا بزواله أبغضه وأحب عدمه والحسد يوجب البغي كما أخبر الله تعالى عمن قبلنا: أنهم اختلفوا من بعد ما جاءهم العلم بغيا بينهم فلم يكن اختلافهم لعدم العلم بل علموا الحق ولكن بغى بعضهم على بعض كما يبغي الحاسد على المحسود. مجموع الفتاوى (10/ 127) "Annabi (saw) ya hada tsakanin Hasada da Kiyayya a cikin Hadisin farko, saboda farko mai hasada yana kin falalar da Allah ya yi ma w...

'YAN UWA, YAU QISSAR IMAMU ABU HANIFA (R) ZAN BA KU

  'YAN UWA, YAU QISSAR IMAMU ABU HANIFA (R) ZAN BA KU Kowa ya san Imamu Abu Hanifa shi ne Limamin Fiqhu na farko a jerin Limaman Fiqhu guda hudu ma'abota Mazhabobin Fiqhu mafi shahara a Duniyar Muslunci. Ya kasance a zamaninsa akwai wani babban Malamin Fiqhu kuma Alkali, wato Muhammad bn Abdirrahman Ibnu Abi Laila. Ya kasance Malamin Fiqhu ne amma Dan Makarantar ra'ayi ne ba Makarantar Hadisi ba. Wannan malami rashin jituwa ta shiga tsakaninsa da Imamu Abu Hanifa, rashin jituwa irin wacce take shiga tsakanin Malamai, saboda sabanin Ijtihadi a wasu Mas'aloli na Addini. To, Ibnu Abi Laila ya kasance a Masallaci yake zama yake yin alkalancinsa, wato a babban Masallacin Kufa. To an ruwaito cewa; wata rana bayan ya tashi daga alkalanci, har ya fita daga Masallacin sai ya ji wata mata tana ce ma wani mutum: "Ya dan Mazinata biyu (babansa da mamarsa)". Wato ta nuna cewa; babansa mazinaci ne, mamarsa ma mazinaciya ce. To sai Alkali Ibnu Abi Laila ya sa aka kira ta. Sa...

Kafin Ka Kafirta 'Yan Hakika, Ka Fara da Tijjani da Inyass

  Kafin Ka Kafirta 'Yan Hakika, Ka Fara da Tijjani da Inyass Wani abu da yake ban takaici shi ne; idan 'Yan Hakika sun zagi Annabi (saw) sai ka ga jagororin Dariqa - Shehunansu da Furofesosinsu da Daktocinsu da tsagerun matasansu - sun fito suna ta kumfar baki, da sunan kare Annabi (saw), alhali a bisa hakika Dariqar kawai suke karewa da Shehunanta. In ba haka ba, Wallahi babu wanda zai yaki Hakika alhali yana cikin Dariqa. Saboda hakikar nan ita ce kololuwar Maqami a cikin Sufanci. Bayan haka, su wadannan Shehunai da ake zagin Annabi (saw) a kansu, wato Shehu Tijjani da Ibrahim Inyas, su ne suka bai wa kawunansu matsayi da Siffofin Allah, suka fifita kawunansu a kan Annabawa da Manzanni a cikin littatafansu, kuma kullum ana karanta wadannan littatafan ga Muridai. To ta yaya Muridi ba zai fahimci ana nuna masa cewa; ya allantar da Tijjani ko Inyas ba?! Tijjaniy da Inyas su suka fara bai wa kawunansu Maqamai na allantar da su. Shehu Tijjaniy ya ce: وما أحد من أوليا الله كلهم ***...