Skip to main content

Posts

Recent posts

SHAIKH JA'AFAR (R) DA 'YAN BOKO AQIDA

SHAIKH JA'AFAR (R) DA 'YAN BOKO AQIDA A kokarinsu na batanci wa Marigayi Shaikh Ja'afar da Da'awarsa ta Sunna da mabiya Sunnan a yau, 'Yan Boko Aqida suna danganta shi da Marigayi Muhammad Yusuf wanda ya kafa Kungiyar Boko Haram, inda suke cewa; ai Muhammad Yusuf din almajirin Shaikh Ja'afar ne, don su nuna cewa; Muhammad Yusuf ya dauki tunanin Boko Haram ne daga Shaikh Ja'afar din. Alhali wasu da suka san Muhammad Yusuf kuma suka san Malam Ja'afar, sun tabbatar da cewa; asali Muhammad Yusuf tafiyar Harkar Gwagwarmayar kifar da Gomnati ya fara yi a karkashin jagorancin Ibrahim El- Zakzaky, wanda daga baya ya yi masa tawaye tare da sauran wadanda suka yi tawaye, bisa zargin shigar da Shi'anci cikin tafiyar, wadanda suka zama Kungiyar JTI, wacce take alakanta kanta da Kungiyar Ikhwan ta Misra. Wanda sai daga baya ne Muhammad Yusuf ya hadu da Malam Ja'afar a bisa tafiyar Sunna ko Salafiyya. A baya - bayan nan, tun bayan bayyanar wani faifan audio na...
  'Yanci a Muslunci shi ne halin da mutum zai kasance mai kaskantar da kai ga mahaliccinsa, cikin mallakar tasarrufin kansa, yana mai zabi cikin aiyukansa matukar bai keta hakkin Allah ko hakkin wani daga cikin bayin Allah ba. Saboda haka ne Muslunci ya ba wa mutum cikakken 'yanci, ta yadda Allah ya halicci mutun ya ba shi 'yanci a fagage masu yawa na rayuwarsa. Allah Madaukaki ya halicci mutum ya ba shi 'yanci da iko da zabi da ganin dama wajen aikata dukkan aiyukansa da zai iya aikatawa, sawa'un aiki ne mai kyau ko kuma aiki ne mummuna. Mutum yana da daman ya bar mummunan aiki don ya samu sakamako da tsira daga azaba a Ranar Lahira, kamar yadda yake da dama da zabi da ikon aikata kyakkyawa don ya samu kyakkyawan sakamako a kansa. Kamar haka Muslunci ya ba ma kowane mutum 'yancin kansa, ta yadda yana da daman yin abin da ya so, kuma ya mallaki duk abin da ya so matukar bai keta hakkin Allah ko hakkin mutane ba. Da wannan Muslunci ya haramta yi ma wani ta'a...

JAFA'I WA ANNABI (SAW) BA MANHAJIN SALAFIYYA BA NE

Kamar yadda Addinin Muslunci yake matsakaici a tsakanin Addinai, haka Mazhabar Salaf Ahlus Sunnati wal Jama'a yake matsakaici a tsakanin sauran kungiyoyi. Salaf Ahlus Sunna a tsakiya suke a dukkan babuka na Addini. Salaf Ahlus Sunna matsakaita ne a babin Tauhidi, tsakanin masu guluwwi da masu jafa'i. Haka a babin matsayin Manzon Allah (saw), tsakanin masu guluwwi da masu jafa'i, da tsakanin masu sakaci (tafridi) da masu zakalkalewa (ifradi). Haka a babin raddi ga 'yan bidi'a, sun kasance tsakanin masu guluwwi da jafa'i, da kuma masu sakaci da tafridi. Haka suke a tsakiya a kowane babi. Wannan shi ne WASADIYYAR AHLUS SUNNA. Saboda haka idan za ka yaki guluwwin Sufaye a game da Annabi (saw), to wajibi ne ka girmama Annabi (saw), bai halasta ka yi jafa'i wa Annabi (saw) ba, da sunan raddi wa guluwwi. Idan za ka yi raddi wa 'yan bidi'a bai halasta ka zalunce su ba, ko ka yi amfani da irin uslubinsu na cin zarafi. Saboda ka'idar Ahlus Sunna ita ce: ba...
  Ni fa na gama gamsuwa cewa; 'Yan Kungiyar Salafiyyun, Malamansu da jahilansu sun jahilci hakikanin Khawarijawa. Ai su Khawarijawa Annabi (saw) ne da bakinsa ya bayyana siffofinsu a fili, daga ciki ya nuna cewa: 1- Sun fi kowa Sallah da Azumi da karatun Alkur'ani, amma maras amfani. 2- Suna "Muruqi" wato suna fita daga Addini. 3- Shi ya sa suke kafirta al'ummar Musulmi gaba daya. 4- Suna kashe Musulmai su bar Kafirai. * Saboda haka ne Annabi (saw) ya zarge su zargi mai tsanani, har ya kwadaitar a kan yakarsu da kashe su. To in ka ce: Malamanmu da suka shahara da da'awar Sunna a Nigeria suna kan tafarkin Khawarijawa to fa kana nufin suna da wadancan siffofi da Annabi (saw) ya yi bayani. Don haka hukuncinsu shi ne a yake su a kashe su. To abin tambaya a nan; yaushe Malamai masu da'awar Sunna a Nigeria suka siffantu da wadancan siffofi har da za a danganta su da Khawarijawa?! Saboda haka da wannan za ka san cewa; duk wanda ya jingina Malamanmu Ahlus Sunna a ...

Shin da Gaske Prof. Maqari ne ya Kirkiri Wadannan Darajoji?

  Shin da Gaske Prof. Maqari ne ya Kirkiri Wadannan Darajoji? Wani ya ce: Kabarin Annabi (saw) ya fi Al'arshi daraja. Wata maganar kuma -wai-: Daren Maulidi ya fi Daren Lailatul Qadr daraja. To lallai duk wanda ya fadi wannan ya jahilci cewa; ita falala ba a tabbatar da ita da dalili na hankali, ko Qiyasi na hankali. Ana tabbatar da falala da daraja ne ta hanyar Nassi. Saboda ita falala da daraja a cikin halitta "Isdifa'i" ne, wato tsantsar zabi ne daga Allah. Allah ya ce: {وربك يخلق ما يشاء ويختار، ما كان لهم الخيرة} [القصص: ٦٨]. {Ubangijinka yana halittar abin da ya ga dama kuma ya zabi abin da ya ga dama (ya fifita shi). Bai kasance suna da zabi ba}. Wannan yake nuna Allah shi kadai yake zabi ya ba da falala da daraja, ba shi da abokin tarayya a cikin haka. To, ta yaya ka san Allah ya zabi Daren Maulidi ya fifita shi a kan Daren Lailatul Qadr? Ta yaya ka san Allah ya zabi Kabarin Annabi (saw) ya fifita shi a kan Al'arshi? Babu hanyar da za ka san haka sai ta ha...
  A bisa hakika babu banbanci tsakanin 'Yan Hakika da Darikun Sufaye. Duk wanda ya san hakikanin Darikun Sufaye ya san sun kunshi Aqidar "Wahdatul Wujudi" (Aqidar komai Allah ne), da kuma Aqidar "Wahdatush Shuhudi" (Aqidar rashin ganin komai sai Allah), da kuma banbanci tsakanin Hakika da Shari'a. Hakika ita ce ta Arifai, kebantattu, Shari'a kuma ta amawa gama garin mutane. Haka kuma a cikin Sufanci akwai Aqidar "Faira", Aqidar nan ta Falsafa da take nuna cewa; komai abu daya ne, komai yana kwarara a cikin komai. Haka kuma in ka dawo cikin wuce gona da iri a hakkin Shehunnai da Waliyyansu, duk wanda ya leka littatafan Malaman Sufaye, ya ga labarun Waliyyai da Shehunnan nasu, kamar Littafin "Jawahirul Ma'aniy", da "Rimahu" da sauransu, zai ga inda suke tabbatar da cewa; Shehunnan nasu suna da dama ta juya Duniya da gudanar da ita, ta hanyar saukar da ruwan sama, da warkas da maras lafiya, kashewa da rayarwa, da cewa; su n...
  Ibnu Rushdi da magabatansa cikin 'yan Falsafa masu dangantuwa ga Muslunci, duk kokarinsu shi ne samar da daidaito tsakanin Falsafa da Muslunci (التوفيق بين الفلسفة والإسلام). Suka yi ta dauko Nassoshin Addinin Muslunci suna dora su bisa ma'ana ta Falsafa, wato ra'ayoyin su Aristotle. To kamar haka, da na duba irin kokarin makarantar Shaikh Sharif Saleh, a cikin Tijjaniyya, sai na ga shi ne kokarin samar da daidaito tsakanin Sufanci da Addinin Muslunci (التوفيق بين التصوف والإسلام). Sun yi rubuce-rubuce don nuna Sufanci shi ne hakikanin Martabar "Ihsani" a cikin Addini, kamar yadda ya zo a Hadisin Jibril (as). Alhali duk wanda ya kalli hakikanin Sufanci, tun karni na 4 zuwa yau, zai tabbatar da cewa; Sufanci wani taron wasu Akidu ne da "Duqus" da aka harhado daga Falsafa da wasu Addinai, irin Kiristanci da Addinan India, kamar Addinin Hindu da Addinin Buda. To wannan makaranta ta su Prof. Maqari, ganin yadda babu yadda za a yi mai hankali da imani, wand...
  IRIN MUNANAN MAGANGANUN INYAS IBRAHIM KAULAHA DAGA INA MATSALAR TAKE ?(3) A rubutunmu na farko da na biyu mun yi bayanin yanda a'kidar allantar da wasu halittu da ma allantar da dukkan komai take da asali acikin 'dari'kar Tijjaniyyah , ta hanyar kawo wani sashe na zantukan Shehu Tijjani wa'danda acikinsu yake tabbatar da wannan munanan a'kidu na kafirci . A yau zamu tsakuro ne daga cikin zantukan Shaikh Ibrahim Inyass wanda acikinsu yake 'kudurce wa'dannan miyagun a'kidu kamar yanda shima Shehu Tijjani ya 'kudurcesu . zamu kasa zantukan Inyass akan wa'dannan miyagun a'kidu zuwa kamar haka : - maganganunsa akan yiwuwar allantuwar bawa - maganganunsa akan allantakar komai -maganganunsa akan allantakar ShehuTijjani . A wannan rubutun zamu tattauna ne akan matashiya biyu na farko , a rubutunmu na gaba kuma sai mu tattauna akan matashiya na 'karshe . Shehu Ibrahim ya gudana a magudana na manya _ manyan jagorori na addinin allantar da halitt...