Skip to main content

Posts

Showing posts from February, 2023

KAFA HUJJA DA HANKALI A ADDINI

  Wani tunani ya watsu a cikin mutane cewa; Manhajin Ahlus Sunnati wal Jama'a ba ruwansa da hankali wajen kafa hujja a kan Mas'alolin Addini da tabbatar da Aqidar Ahlus Sunna, don haka Ahlus Sunna ba sa ba da muhimmanci ga hankali da tunani, kawai makauniyar biyayya suke yi wa magabata ido rufe, kamar masu bin Addinin iyaye da kakanni. Wadanda suke dauke da wannan tunani bangare biyu ne: 1- Wadanda suka saba Manhajin Salaf, mabiya hanyoyin Falsafa cikin 'Yan Boko Aqida, wadanda suka rudu da rayuwar Turawa, mabiya Ilmul Kalam; Mu'utazilawa da Asha'ira, da masu ta'assubanci cikin mabiya Fiqhu da Qiyasi, wadanda suke sukan Ahlus Sunna da rashin tunani da fahimta da rashin aiki da hankali wajen kafa hujja, da siffanta su da rashin Fiqhu. 2- Wasu daga cikin masu bin Mazhabar Salaf, wadanda suka yi zaton hanya daya ce kawai ta kafa hujja a Mazhabar Salaf a kan Mas'alolin Addini, wato hanyar Nassi da Naqali kawai, don haka suka yi watsi da hanyar kafa hujja da dali...

ILIMI YA FI MULKI DA'DI!

  AL- IMAMUZ ZAHABIY YA KAWO A CIKIN "SIYAR" 'DINSA, A TARJAMAR IMAMU 'DABARANIY (MAI MA'AJIM GUDA 3): ABUL HUSAIN, AHMAD BN FARIS AL- LUGAWIY (MAI LITTAFIN MAQAYISUL LUGHAH) YA CE: سمعت الاستاذ ابن العميد يقول: ما كنت أظن أن في الدنيا حلاوة ألذ من الرئاسة والوزارة التي أنا فيها، حتى شاهدت مذاكرة أبي القاسم الطبراني وأبي بكر الجعابي بحضرتي، فكان الطبراني يغلب أبا بكر بكثرة حفظه، وكان أبو بكر يغلب بفطنته وذكائه حتى ارتفعت أصواتهما، ولا يكاد أحدهما يغلب صاحبه، فقال الجعابي: عندي حديث ليس في الدنيا إلا عندي، فقال: هات، فقال: حدثنا أبو خليفة الجمحي، حدثنا سليمان بن أيوب، وحدث بحديث، فقال الطبراني: أخبرنا سليمان بن أيوب، ومني سمعه أبو خليفة، فاسمع مني حتى يعلو فيه إسنادك، فخجل الجعابي، فوددت أن الوزارة لم تكن، وكنت أنا الطبراني، وفرحت كفرحه، أو كما قال. "NA JI USTAZ IBNUL AMID (WAZIRIN RUKUNUD DAULA AL- HASAN BN BAWAIH AL- DAILAMIY, SARKIN DAULAR BUWAIHIYYA WACCE AKA YI TA A IRAQI) YANA CEWA: DA BAN TA'BA ZATON A DUNIYA AKWAI ABIN DA YA FI MULKI DA WAZIRANCI D...

MATAKAN BIDI'O'I

  Tambaya: "shin bid'ah akwai babba akwai karama?". Amsa: Bidi'a suna ne na jinsin dukkan abin da aka kirkira aka shigar da shi cikin Addinin da Manzon Allah (saw) ya zo da shi, alhali ya saba ma Qur'ani da Sunna da Ijma'i. Sawa'un wannan abin ya zama kishiyar asali daga cikin asalai na Addini, wato manyan lamuran Addini, ko kuma reshe ne daga cikin rassansa, wato kananan lamura na Addini. Shaikhul Islami Ibnu Taimiyya ® ya ce: مما ينبغي أيضا أن يعرف أن الطوائف المنتسبة إلى متبوعين في أصول الدين والكلام: على درجات منهم من يكون قد خالف السنة في أصول عظيمة ومنهم من يكون إنما خالف السنة في أمور دقيقة. مجموع الفتاوى (3/ 348) Sai ya nuna cewa; saba Sunna ya kasu kashi biyu: (1) Saba Sunna a Manyan Tushen Sunna, kamar Siffofin Allah da Qaddara da Mas'alar Imani, da Khalifanci da Falalar Sahabbai. (2) Saba Sunna a kananan abubuwa. Saboda haka bidi'o'i da 'Yan Bidi'a ba a daraja da matsayi daya suke ba, wata Bidi'ar ta fi wata. Shi ya sa ak...

Tushen ilhadi

  Tushen Ilhadi shi ne kalubalantar abin da Annabi (saw) ya zo da shi na Alkur'ani da Sunna da ra'ayi da tunani da hankali da Falsafa. Wannan ya sa ba za ka taba samun wanda yake kalubalantar Hadisan Annabi (saw) da ra'ayoyinsa da yake zayyana su da sunaye kala-kala, da sunan ilimi ko zurfin tunani ko hazaka ko kaifin kwakwalwa da kaifin basira face yana kiyayya ga abin da ya saba ra'ayinsa cikin Hadisan Annabi (saw), har ya wayi gari yana fatan da Annabi (saw) bai fadi Hadisin ba. Ta yadda da zai samu daman goge Hadisin daga Sahihul Bukhari da Muslim to da zai yi. Al-Subkiy ya ambaci maganar Ahmad bn Sinan a cikin littafinsa ya ce: ليس في الدنيا مبتدع إلا يبغض أصحاب الحديث وإذا ابتدع الرجل نزعت حلاوة الحديث من قلبه طبقات الشافعية الكبرى للسبكي (2/ 6) "A Duniya babu wani dan bidi'a face yana kin Malaman Hadisi, idan mutum ya kirkiri bidi'a za a cire zakin Hadisi a zuciyarsa". Shi ya sa wani babban gungume cikin 'Yan Bidi'a magabata ya ce: Idan ...

ZABEN SHUGABAN DA YA FI DACEWA

  Zaban shugaba a cikin mutane yana da matukar muhimmanci a rayuwarsu ta Addini da rayuwarsu ta Duniya. Rayuwar mutane ta Addini ba ta cika sai da kyakkyawan shugabanci da zai kare manufofin Shari'a, na kare Addini ta hanyar umurni da kyakkyawa da hani ga mummuna da tsayar da haddi da tsayar da adalci da mayar da hakkoki ga ma'abotansu da Jihadi saboda Allah, da kare rayuka da hankulan mutane. Haka in ka dawo bangaren rayuwar Duniyar mutane, rayuwar ba ta inganta sai da ingantaccen shugabanci da zai samar da tsaro da cigaban kasa ta hanyar inganta harkar ilimi da bunkasa harkar noma da kasuwanci da habaka tattalin arziki da samar hasken wutan lantarki da makamashi da kuma bunkasa harkar kimiyya da fasaha da zai inganta harkar kiwon lafiya da kere-kere, da samar da kayan more rayuwa da duk abin cigaban rayuwa yake bukata. To shi shugabanci yana bukatar manyan siffofi guda biyu: 1- Karfin iko 2- Rikon amana. Sai kuma ka kara da wanda zai kare maka Addininka da rayuwarka. Don haka...

SA'BANI A TSAKANIN AHLUS SUNNA A KAN K'ANANAN MAS'ALOLIN ADDINI BAI KAI YA ZAMA SANADIN RABUWAN KAI BA!!!

  IBNU ABIL IZZ AL- HANAFIY (R) YA FA'DA A CIKIN LITTAFINSA "SHARHU'D 'DAHAWIYYA", INDA YAKE MAGANA A KAN HUKUNCIN BIN FAJIRI KO 'DAN BIDI'A SALLAH: إن مصلحة الجماعة والائتلاف، ومفسدة الفرقة والاختلاف، أعظم من أمر المسائل الجزئية. YA CE: "LALLAI MASLAHAR DA KE CIKIN HA'DA KAI DA JAMA'A, DA KUMA 'DINKE 'BARAKA, DA 'BARNAN DA KE CIKIN RABUWAR KAI DA SA'BANI YA FI GIRMA FIYE DA LAMARIN K'ANANAN MAS'ALOLI". * WANNAR MAGANAR TA SHAIKHUL ISLAM IBNU TAIMIYYA (R) CE A CIKIN "JAMI'UL MASA'IL 5/ 274". A CAN K'ARSHEN MAGANARSA SAI YA CE: إن الاجتماع والائتلاف مما يجب رعايته وترك الخلاف المفضي إلى الفساد. "LALLAI HA'DIN KAI DA 'DINKE 'BARAKA YANA DAGA CIKIN ABUBUWAN DA YA WAJABA A KIYAYE SHI A KULA DA SHI, KUMA A BAR SA'BANIN DA ZAI KAI ZUWA GA 'BARNA". WANNAN SHI YAKE NUNA MANA CEWA; BAI KAMATA AHLUS SUNNA SU MAI DA K'ANANAN MAS'ALOLI (MAS'ALOLIN AIYUKAN IBADA, W...

IBNU TAIMIYYA YA FI KOWA RADDI WA 'YAN BIDI'A, AMMA KUMA DUK DA HAKA YA FI KOWA YI MUSU UZURI DA ADALCI

  Abu ne sananne Shaikhul Islami Ibnu Taimiyya (r) yana daga cikin Imaman Ahlus Sunna wal Jama'a, wanda a bayansa har zuwa yau ba a samu wanda ya kai shi girmamawa da bin Nassoshin Al- Qur'ani da Sunna da Tafarkin Salaf (magabata) ba. Wannan ya sa ba a samu wanda yake kare Sunna da tafarkin magabata kamarsa ba, shi ya sa ya fi kowa raddi ma wadanda suka saba tafarkin Annabawa, tun daga kan 'Yan Falsafa, Mulhidai, Mushrikai da Majusawa, Yahudawa da Kiristoci da dukkan dangogin kungiyoyin 'yan bidi'a. Amma abin mamaki, duk da haka ya kasance mutum ne mai adalci saboda binsa ga Al- Qur'ani da Sunna da tafarkin Salaf, shi ya sa ba ya yin kudin goro wajen yanke hukuncinsa ga 'yan bidi'a, a'a, kowa yana yi masa hukunci ne gorgodon girman bidi'arsa da halinsa na bin son rai ko kuskure, wanda kuma yake bukatar azuri yana yi masa uzuri tare da yi masa fatan samun gafara a kan kuskuren nasa. Ibnu Taimiyya yana magana a kan wadanda suka hada ra'ayin ...

WANENE MALAMIN 'YAN FALSAFA (PHILOSOPHERS) NA FARKO?

  Kasancewar hakikanin Falsafa shi ne dogaro a kan hankali zalla wajen sanin hakikanin lamura da yi musu hukunci, in mun duba za mu ga Iblis shi ne farkon wanda ya fara zuwa da Nazariyyar gabatar da hankali a kan komai wajen yanke hukunci. Ya yi amfani da wannar Nazariyya ce (theory) inda ya gabatar da hankalinsa a kan maganar Allah Madaukaki ya yanke hukunci da ya saba umurnin Allah. Shi ne farkon wanda ya fara kalubalantar maganar Allah ya rushe ta bisa dogaro ga hankalinsa, bisa Nazariyyar: hankali shi ne gaba da Nassi in an samu sabani a tsakaninsu. Hakan ya faru ne a lokacin da Allah ya umurce shi da yin Sujada ga Annabi Adamu (as), sai ya kalubalanci Allah da wata ka'ida ta Falsafa mai doriya biyu kamar haka: 1- Ni da wuta ka halicce ni, shi kuma (Annabi Adamu) da tabo ka halicce shi, wuta kuwa ta fi tabo daraja. 2- Don haka wanda aka halicce shi da wuta ya fi wanda aka halicce shi da tabo daraja. Natijar wannar Qadhiyya ita ce: Ni na fi Adamu daraja, don haka ni ba zan yi ma...

haqiqanin ilimi shine tsoron Allah

Haƙiƙanin Ilimi shi ne Jin Tsoron Allah Asali ilimin Shari'a aiki ne na ibada ma Allah Maɗaukaki da hanyar neman yardarsa. Wannan shi ne abin da Nassoshin Alƙur'ani da Sunna suka yi nuni a kansa, kuma a wannan matsayi magabatan al'umma Sahabbai da Tabi'ai da Limman ilimi da Addini suka ɗauki ilimin. Don haka mu ma a wannan matsayi ya kamata mu ɗauki ilimin na Shari'a, a matsayin aiki na ibada da neman kusaci a wajen Allah da neman yardarsa. Allah ya ce: {وَاتَّقُوا اللَّهَ وَيُعَلِّمُكُمُ اللَّهُ } [البقرة: 282] "Ku ji tsoron Allah sai Allah ya ba ku ilimi". Ya ce: {إِنَّمَا يَخْشَى اللَّهَ مِنْ عِبَادِهِ الْعُلَمَاءُ } [فاطر: 28] "Lallai Malamai ne kaɗai suke jin tsoron Allah a cikin bayinsa". Saboda haka ilimi ba ya rabuwa da tsoron Allah. Don haka mai karatun da ba ya jin tsoron Allah shi ba Malami ba ne. Saboda haka abin mamaki ne a yau yadda wasu suka mayar da ilimin Shari'a ya zama abin ado da alfahari da neman girma da neman suna da sh...