Akwai wata magana ta Ibnu Taimiyya wacce wasu suka samo, suke yadawa don daure gindi ma wata mummunar Akidar 'yan bidi'a, ta Guluwwi game da Annabi (saw), ta cewa an halicci Duniya ne don Manzon Allah. To, asali 'yan bidi'a suna kafa hujja a kan wannar Akida ta Bidi'a ne da Hadisan da duka Hadisan karya ne, kamar yadda yake sananne a wajen Malamai, har shi Ibnu Taimiyyan ya tabbatar da haka. Don haka sai suka samo wata magana ta Ibnu Taimiyya ake yada ta a matsayin shubuha, don a yi ilzami ma Wahabiyawa da ita. Alhali duk wanda ya yada wannar magana bisa wancan Maqsudi na 'yan bidi'a, to bai fahimci maganar Ibnu Taimiyya ba. Don abin da maganarsa take nufi shi ne: Ibnu Taimiyya ya danganta hikimar halittar Duniya ne ga Annabi (saw) a babin FALALARSA A KAN MUTANE (الأفضلية), BA A BABIN KHUSUSIYYA (الخصوصية) BA. WATO BA ABU NE DA YA KEBANTA DA ANNABI (SAW) SHI KADAI BA. Ma'ana; bisa nazari cikin Ayoyin Alkur'ani za a ga cewa: Allah ya halicci halittu n...
Karatuttukan addinin musulunci da harshen Hausa