YADDA AKE YIN MAN KWAKWA Da kuma amfaninsa. Daga shafin Sunnah Medicine masu yin Ruq'yah da harhada Magungunan Musulunci. https://www.facebook.com/sunnahmedicinepage/ Lambar waya 08162600700, 08134434846. Yadda ake hada Man Kwakwa:- Ababe da za’a bukata •Kwakwa •Ruwa Yadda za a hada. A samu Kwakwa mai kyau, sai a 6are 6won a kankare bayan kwakwar ya rage farin kawai, sannan a yayyanka ta kanana saboda ta yi saukinmarkadawa. A zuba ruwa da dan dama a cikin blandar sai ahada da yankakkiyar kwakwar sai a markada har sai markaden ya yi laushi sosai. A sami a bin tatar kamu a tace ruwan kwakwarsosai, za a ga ruwan kamar madara. Za’a iya ajiye markadadden ruwan kwakwa nakwana daya ga wadda ba ta da firinji ko kuma asaka shi a firinji domin ruwan ya hadu sosai. Bayan kwana daya za a ga madarar kamarkindirmo a saman kwano. Sai a kwashe wannan madarar da aka tace a zuba ta a cikin tukunyar suyar sai a dora tukunyar a kan wuta, haka za a yi tajuyawa da cokali har sai wannan madarar ta komaka...
Karatuttukan addinin musulunci da harshen Hausa